IQNA

22:08 - December 30, 2017
Lambar Labari: 3482252
Bangaren kasa da kasa, majalisar musulmin kasar Kenya ta nuna damuwa matuka tare da yin kakkausar suka dangane da cutar da dalibai mata musulmi da ske saka hijabi.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin yada labarai na hivisasa ya habarta cewa, Abdullahi Salat shugaban majalisar muuslmin kasar Kenya a cikin wani bayani ya nuna damuwa tare da yin kakkausar suka dangane da cutar da dalibai mata musulmi da ske saka hijabin musulunci a cikin jami’oi.

Bayanin yace babu wani dalili da zai saya a dauki karan tsana  adora kan dalibai mata musulmi a jami’oi saboda saka hijabi da suke yi a matsayinsu na musulmi ‘yan kasa da suke da hakki kamar kowane dan kasa.

Salat ya ce awai abubuwa da dama da suka faru da dalibai muuslmi mata da daman a izgili da cutarwa, saboda sun saka lullubi a kansu.

Ya ce suna yin kira ga jami’oi da su dauki kwararan matakai na kare hakkokin dalibai muuslmi da ske saka lullubi bisa koyarwar addininsu, wanda kuma kundin tsarin mulkin kasar ya yarje musu yin hakan, idan kuma ba haka ba za su dauki mataki na shari’a domin kalubalantar irin wannan mummunar dabi’a.

A shekara ta 2016 ce kotun kolin kasar Kenya ta fitar da dokar da ke bayar da dama ga dalibai musulmi su saka lulubi a cikin makarantu da jami’oi na kaar Kenya.

Kasar Keya na gabashin Afirka, kuma musulunci ya isa wasu yankunan kasar ne tuna  cikin karni na uku hijira kamariyya, kuma fiye da kashi 15 cikin dari na mutanen kasar muuslmi ne.

3677481

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: