IQNA

Saudiyya Ta Kashe Fararen Hula A kasar Yemen

16:36 - December 31, 2017
Lambar Labari: 3482256
Bangaren kasa da kasa, a hare-haren da jiragen saman yakin masarautar Saudiyya suka kaddamar a yammacin jiya a kan lardin Hudaidah na kasar Yemen, fararen hula talatin ne suka rasa rayukansu, wasu da dama kuma suka jikkata.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, kamfanin dillancin labaran saba'a ya watsa rahoton cewa; A harin wuce gona da iri da jiragen yakin Saudiyya suka kaddamar a kan gidajen jama'a a yammacin jiya a lardin Hudaidah Umran, fararen hula talatin sun rasu, mafi yawancinsu mata ne da kananan yara, yayin da wasu da dama suka samu raunuka.

Wadannan hare-hare na Saudiyya na zuwa ne kwana daya bayan rahoton da hukumar kula da kananan yara ta duniya ta fitar da ke cewa, daga shekara ta 2015 zuwa Disamban wannan shekara mai karewa, Saudiyya ta kashe kananan yara fiye da dubu biyu a Yemen ta hanyar kai hare-hare da jiragen yaki a kan gidajensu.

Bayanin ya kara da cewa baya ga kananan yara fiye da dubu biyu da suka mutu ta hanyar hare-haren Saudiyya, wasu dubban kuma sun mutu ta hanyar jefa su cikin yunwa da hana kai musu tallafin abinci da magunguna.

3677877

 

 

captcha