IQNA

Kungiyar Mata Musulmi A Najeriya Ta Jaddada Wajabcin ‘Yancin Saka Hijabi

23:20 - February 01, 2018
Lambar Labari: 3482354
Bangaren kasa da kasa, kungiyar mata musulmia  Najeriya ta jaddada wajabcin bayar da ‘yancin saka lullubi ga mata musulmi a kasar.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na Anatoli cewa, malama Ni’imatullah Abdulkadir shugabar kungiyar mata musulmi mai suna Almuminat ta bayyana cewa, wajibi ne a bayar da ‘yanci ga mata musulmi su saka hijabi a kasar ba tare da tauye hakkins ba.

Ta ce a wannan shekara ma kamar sauran shekarun da suka gabata, za su gudanar da tarukan ranar hijabi ta duniya, kuma za su gabatar da jawabai da ke bayyana maharsu kan wannan batu, kamar yadda tace za su gabatar da wata bukata ga majalisa domin samar da wani daftarin doka, wanda zai ba mata musulmi ‘yancin saka lullubi a duk inda suke a Najeriya ba tare da wani matsin lamaba a kansu ba.

Ta ce taken ranar hijabi a bana a Najeriya shi ne “hijabi hakkina ne” wanda yayi daidai da bukatar ad suke son gabatarwa a gaban majaliar dokokin Najeriya.

A farkokn kowane watan fabrairu mata musulmi suna gudanar da tarukan ranar hijabi ta duniya, inda  abana kasashe 140 ne ake gudanar da wadannan taruka.

3687438

 

 

 

 

captcha