IQNA

Shiri Mai Taken Monolog Dangane Da Hijabi A Texas

23:10 - February 06, 2018
Lambar Labari: 3482370
Bangaren kasa da kasa, musulmi mata za su gudanar da wani shiri mai suna monolog kan hijabi a jahar Texas da ke kasar Amurka.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin yada labarai na dailytexanonline ya bayar da rahoton cewa, a ranar 2 ga watan Maris musulmi mata za su gudanar da wani shiri mai suna monolog kan hijabi a jahar Texas da ke kasar Amurka tare da halartar kungiyoyi daban-daban.

Hanan Hashem daya daga cikin wadanda za su shirya gudanar da wanann taro ta bayyana cewa, manufar yin hakan ita ce gyara mummuna tunanin da wasu suke da shi a kan hijabin musulunci.

Ta ce a lokacin da take karatu a jami’a ta shirya irin wadannan taruka, kuma sun yi tasiri matuka, a kan a wannan karo ta yanke shawara tare da wasu abokanta musulmi kan ci gaba da yin hakan.

Haka nan kuma ta yi ishara da irin matsalolin da wasu daga cikin msuulmi suke fuskanta a halin yanzua  cikin wannan jaha da ma wasu jahohi na kasar Amurka, musamman ma mata daga cikinsu wadanda suke saka hijabi.

A taron dai za a bayar da dama gam asana domin su bayyana irin hikima da take tattare da hijabi da kuma abin da ya sanya musulunci yayi umarni da shi.

3689069

 

 

captcha