
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Bahrain yaum cewa, a jiya an gudanar da zaman taron manema labarai a wani dakin taro a majalisar dokokkin Birtaniya dangane da halin da ake cikin a kasar Bahrain kan cin zarafin bil adama da masarautar kama karya ta kasar key i.
Zaman taron dai ya hada masu fafutuka da kuma ‘yan jarida gami da wasu daga cikin ‘yan majalisar dokokin Birtaniya, inda aka yi bayani kan irin matakan da masarautar kama karya ta Bahrain take ci gaba da yin amfani da karfin soji wajen murkushe ‘yan adawar siyasa da sauran fararen hula masu neman hakkokinsu da a ka murde musu.
Masarautar kama karya tana yin amfani da dalilai na siyasa da banbancin mazhaba wajen cutar da mutanen kasar, musamman ma mabiya mazhabar shi’a, wadanda su ne fiye da kashi tamanin na al’ummar kasar, yain da wahabiyawa wadanda su ne ‘yan tsiraru a kasar su ne suke mulki, tun bayan da turawan mulkin mallaka na Birtaniya suka mika musu ragamar tafiyar da kasar.
Dukkanin cin zarafin da masarautar kama karya ta Bahrain key i kan fararen hula da ‘yan siyasa da masu fafutuka, da hakan ya hada da kisa da dauri da kora da kwace takardun izinin zama dan kasa ga ‘yan asalin kasar, amma gwamnatin Birtaniya na ci gaba da marawa mara ma masarautar ta Bahrain baya, lamrin da hatta mutane Birtaniya suke ganin haka matsayin wani nau’in munafuci irin na gwamnatin Birtaniya.