IQNA

Kamfen Wayar Da Kan Amurkawa Dangane Da Addinin Musulunci

22:38 - March 02, 2018
Lambar Labari: 3482445
Musulmin birnin Chattanooga na jahar Tennessee a kasar Amurka suna gudanar da wani kamfe na wayar da kan Amurkawa kan addinin muslunci.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Shafin yada labarai na chattanoogapulse.com ya bayar da rahoton cewa, sakamakon irin matakan da musulmi suke dauka a jahar Tennessee suna kara samun karbuwa a tsakanin jama'a.

Hamamd Amin shi ne shugaban wannan kamfe, ya bayyana cewa sun kirkiro da wannan shiri mai taken (mu gana da makwafta) domin ganawa da sauran jama'a wadanda ba musulmi ba, tare da yi musu bayani kan musulunci da kuma amsa tambayoyin da suke shige musu duhu a kan wannan addini.

Ya ce sukan gayyaci mutane a masallatai da cibiyoyin musulunci gudanar da wannan taro na wayar da kai, inda akan yi bayani daga bisani kuma a bayar da damar yin tambayoyi.

Haka nan kuma aka n nuna musu wasu abubuwa na musulunci, da suka hada kwafin kur'ani da kuma bayanin wasu ayoyin da ke cikinsa.

Ya kara da cewa hkika wannan lamari ya yi tasiri matuka, domin mutane fiye da dubu biyu ne suka zo wurin kuma suka ji bayanan da aka yi kuma aka amsa musu tambayoyinsu.

Bayan kamala taron a cewarsa, wasu da yawa wadanda ba musulmi sun yi ta kira suna nuna rashin jin dadinsu dangane da rashin samun halarta.

3695816

 

captcha