Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin jaridar vanguard da ake bugawa a Najeriya ya bayar da rahoton cewa, Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne a cikin jawabinsa a yayin taron rufe gasar kur’ani mai tsarki ta kasa karo na talatin da biyu da aka gudanar a birnin katsina na jahar katsina da ke arewacin Najeriya.
Ya ce kur’ani ya koyar da mu yadda za mu yi hulda da cudanya da kowa, kamar yadda ya koyar da mu yadda za mu mu’amala hard a mutanen da ba musulmia cikin aminci da gaskiya.
Haka nan kuma shugaba Buhari ya bayyana cewa, kur’ani mai tsarki tare da dukkanin sauran littafai da suka sauka daga sama suna yin kira ne zuwa ga zaman lafiya da girmama juna.
An kamala gasar wadda aka gudanar a birnin Katsina tare da halartar makaranta kur’ani daga jahohi daban-daban na Najeriya.