IQNA

Masar: Taron kasa Da Kasa Kan Adana Kayan Tarihin Musulunci

21:07 - March 05, 2018
Lambar Labari: 3482453
Bangaren kasa da kasa, za a gudanar da wani babban taro na kasa da kasa a birnin Alkahira na kasar Masar kan adana kayan tarihin musulunci.

Masar: Taron kasa Da Kasa Kan Adana Kayan Tarihin MusulunciKamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin yada labarai na sadal balad ya bayar da rahoton cewa, taron wanda za a fara shi a ranar Laraba mai zuwa, zai samu halartar manyan malamai da masana daga kasashe kalla guda 20, inda za a gabatar da makaloli a kan kayan tarihin musulunci da kuma tasirin wanzuwarsu.

Kasashen da za su halarci wannan taro kuwa sun hada da Iraki, Indonesia, Morocco, Kuwait, Aljeriya, India, Denmark, UAE, Lebanon da sauransu.

Wannan taro dai jami'ar Azhar ce za ta dauki nauyinsa, tare da hadin gwiwa ma'aikatar kula da harkokin addini ta kasar Masar.

Babbar manufar taron dai ita ce hankoron farfado da kishin raya tarihin musulunci da duk wani abu da ya danganci hakan, da kuma kara zurfafa bincike a wannan fage.

3697031

 

 

 

 

captcha