IQNA

Za A Kafa Kwamitin Masu Hidima Ga Kur’ani Na Duniya A Masar

23:09 - March 26, 2018
Lambar Labari: 3482512
Bangaren kasa da kasa, za a kafa wani kwamiti na masu hidima ga kur’ani mai tsarki na duniya a kasar Masar.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ministan ma’aikatar kula da harkokin addini ta kasar Masar Muhammad Mukhtar Juma’a ya bayyana cewa, ana shirin kafa wani kwamiti na masu hidima ga kur’ani mai tsarki na duniya.

Ministan ya bayyana hakan ne bayan bude gasar kur’ani kur’ani ta duniya a kasar Masar da ke samun halartar makaranta da mahardata kur’ani daga sassa na duniya.

Ya ce wannan kwamiti aikinsa shi ne gudanar da ayyuka da suka shafi kur’ani da sanya ido a kan duk wasu lamurra da suka danganci kur’ani a matsayi na duniya, ta yadda zai zama yana da mambobi daga dukkanin kasashen musulmi da na larabawa da ma wasu daga cikin kasashen duniya, domin musulmi su samu wakilci a cikinsa  aduk inda suke.

Daga karshe ya bayyana gasar da ke gudana Masar da cewa babbar dama da za a yi amfani da ita wajen girka wannan kwamiti, wanda za a sanar da tsare-tsarensa da zaran an kammala gasar.

3701903

 

 

 

 

 

 

captcha