Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin yanar gizo na bawwaba News cewa, a gefen zaman gasar kur'ani karo na ashirin da hudu da aka gudanar a Masar, an kuma gudanar da wani zaman nazari kan mas'alolin ilimin addini.
Usama Al'ab shugaban kwamitin kula da harkokin addini a majalisar dokokin kasar gami da tsohon shugaban cibiyar Azhar, su ne suka jagoranci zaman taron.
An fara gudanar da zaman gasar ne tun ranar Asabar da ta gabata, an kuma kamala gasar a jiya laraba.
Mahardatan kur'ani 66 ne daga kasashe 50 da kuma alkalan gasar kur'ani su goma suka halarci wannan gasa ta kasa.