Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, rundunar sojin kasar Syria ta bayyana yankin Ghouta da cewa a halin yanzu ya fita daga hannun 'yan ta'addan wahabiyawan takfiriyya, tare da dawo da doka da oda da kuma kubutar da dubban daruruwan fararen hula da 'yan ta'addan suka rike a yankin a matsayin wata garkuwa.
Bayanin ya kara da cewa, an cimma yarjejeniya tare da 'yan ta'addan Jaish Islam wadanda Saudiyya ta kafa kuma take daukar nauyinsu, wadanda suka yi taurin kai dangane da ficewarsu daga unguwar Doma inda suka kafa tungarsu, sojojin Syria sun ba su wa'adi ya kare a jiya kan cewa ko dai su fita ko kuma a fitar da gawawwakinsu, inda su da masu daukar nauyinsu suka amince kan cewa za su fice zuwa yankin Jaranlus da ke kan iyaka da Turkiya.
'Yan ta'addan sun amince kan cewa ba za su fita da manyan makamai da kuma matsakaita makamansu ba, amma za su fita da kanan makamai da ke a hannusu salun alun, yayin da sauran makaman baki daya za a mika su ga rundunar sojin kasar Syria.