IQNA

Cibiyar Ibrahimi Na Koyar Da yara Ilmomin Kur'ani A Ingila

23:47 - April 10, 2018
Lambar Labari: 3482557
Bangaren kasa da kasa, cibiyar Ibrahimi wata cibiya ce da take bayar da gudunmawa wajen horar da yara kan tarbiya ta kur'ani wadda aka samar tun 2009.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin yanar gizo na iric.org ya habarta cewa, cibiyar (abrahamic foundation) an gina ta ne tun 2009 da nufin samar da makaranta kur'ani da kuma malaman kur'ani da za su bayar da gudunmawa wajen yada koyarwarsa a Birtaniya da turai.

Babban aikin wannan cibiya dais hi ne koyar da kur'ani da kuma duk wasu ilmomi da suka shfi kur'ani a matakin farko da matsakaici, wanda kuma ake fatan a nan gaba za a kai ga matakin kwrewa.

Kasar Birtaniya dai na daga cikin kasshen da musulmi suke fuskantar matsaloli a halin yanzu daga wasu masu tsatsauran ra'ayin kin jinin muslunci da musulmi.

Wannan yana faruwa ne sakamakon karuwar ayyukan ta'addanci da wasu masu dauke da akidar wahabiyanci suke aikatawa da sunan addinin muslucni, wanda hakan yake ci gaba da bata fuskar muslucni a idon duniya.

3704683

 

 

 

captcha