IQNA

Gangamin Yin Kira Da A Saki Sheikh Zakzaky A Kasashe Daban-Daban

23:52 - April 16, 2018
Lambar Labari: 3482574
Bangaren kasa da kasa, ana gudanar da gangami a kasashe daban-daban da suka hada da Turkiya, Switzerland, Pakistan Birtaniya domin yin kira da a saki Sheikh Zakzaky.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin yada labarai na Lu'ulu'a ya bayar da rahoton cewa, a cikin makon nan ana gudanar da gangami a kasashe daban-daban da suka hada da Turkiya, Switzerland, Pakistan Birtaniya domin yin kira ga gwanatin tarayyar Najeriya da a saki Sheikh Zakzaky da ake tsare da shi.

Wannan gangami da jamaa suke gudanarwa a kasashen duniya daban-daban sakamako na kiran da kungiyar kare hakkokin musulmi a kasar Ingila ta yi ga kungiyoyin musulmi daban-daban a nahiyar turai, kan su matsa lamba kan majalisar dinkin duniya domin ganin an sakin malamin

Tun a karshen watan Disamban shekara ta 2015 ne dai jami'an sojin Najeriya suka kaddamar da farmaki a kan gidan malamin a zaria da kuma cibiyar da suke gudanar da tarukan addini, inda sojojin suka kasha daruruwa daga cikin mabiyansa da suka hada har da 'ya'yansa uku.

Tun daga lokacin kuma ake ci gaba da tsare shi tare da mai dakinsa, kuma magoya bayansa na ci gaba da gangami domin neman a sake shi kamar yadda kotu ta bayar da umarni, amma gwamnatin Najeriya ba ta sake shi ba.

3705927

 

 

 

 

captcha