Kamfanin dillancin labaran iqn aya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Aldastur cewa, Dokta Ahmad Tayyid shugaban cibiyar Azhar a lokacuin da yake ganawa da shugaban Indonesia ya bayyana cewa yada sasauci tsakanin musulmi shi ne hanyar warware matsalolinsu musamman a wannan zamani.
Ya ci gaba da cewa ko shakka babu rashin fahiomtar addini na daya daga cikin abubuwan da suka kara kawo matsaloli tsakanin musulmi ta hanyar yaduwar tsatsauran ra'ayi bisa jahilci, ta yadda wani daga zai kafirta musulmi ba tare da shi ya san musulunci yadda ya kamata.
Dangane da yadda za a magance wannan matsala, shugaban na cibiyar Azhar ya bayyana cewa dole ne malamai daga cikin musulmi su mike tsaye domin wayar da kai da kuma samar da hanyoyi na hada kan musulmi da kuma yada fahimta ta sassauci da fahimtar juna.