IQNA

23:55 - May 01, 2018
Lambar Labari: 3482622
Bangaren kasa da kasa, shugaban kasar Amurka Donald Trump yaki neman uzuri dangane da kalaman kin jinin musulmi da ya yi a lokacin yakin neman zabe.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, tashar talabijin ta CNN ta bayar da rahoton cewa, a lokacin da aka tambayi shugaba Trump ko zai nemi uzuri daga muuslmi kan kalaman batuncin da ya yi ga musulmi a lokacin yakin neman zabe.

Daga cikin irin matakan da shugab Trump ya alokacin yakin neman zabe akwai batun cewa idan har ya lashe zabe zai hana musulmi shiga cikin Amurka.

Bayan da ya ci zaben ya aiwatar da wanann doka a aikace, inda ya kafa dokar hana shigar musulmi cikin Amurka daga wasu kasashe, yayin da kuma wasu da ya yi wa barazana ya kafa musu sharuddan bayar da daruruwan biliyoyin daloli.

Trump dai shi ne shugaban Amurka na farko da ya fito ya nuna tsananin kiyayayrsa ga musulmi tun kafin ya lashe zabe, kamar yadda kuma ya kara tsananta kiyayayrsa ga musulmi bayan lashe zaben.

3710894

 

 

 

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: