Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafi Altagyir cewa, wakilin Yemen a gasar Malaysia Dokta Ihab Muhammad Ibrahim Ilyan ya kai ga mataki da za a fitar da wadanda za su kara daga karshe.
Bayanin ya ce wannan gasar kur'ani mai tsarki tana samun halartar makaranta da mahardata daga kasashen duniya daban-daban.
Haka nan kuma wanann gasar ta Malaysia ita ce gasar kur'ani mafi jimawa a duniya inda ta cika shekaru 60 da faraway, kuma an fara gudanar da ita ne a lokacin fira minister Tanko Abdulrahman Potra.