IQNA

23:46 - May 11, 2018
Lambar Labari: 3482647
Bangaren siyasa, jagoran juyin juya halin musulunci a Iran ya ziyarci kasuwar baje kolin littafai ta duniya da ke gudana a binin Tehran.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a yau Juma’a jagoran juyin juya halin musulunci a Iran Ayatollah sayyid Ali Khamenei ya ziyarci kasuwar baje kolin littafai ta duniya da ke gudana a binin Tehran tare da rakiyar wasu daga cikin jami’ai.

A lokacin da yake duba runfunan littafai tare da rakiyar Saehi ministan yada al’adu, jagoran ya duba rumfuna kimanin guda 50, tare da duba irin abubuwan da suka kawo na daga littafai.

Jagoran ya bayyana cewa; littafi a koda yaushe yana a matsayin rayayyen malami, kuma babu abin da zai cike gurbin ittafi, domin kuwa ta hanyarsa ne ake samar da dukkanin lmomi wanda masana suka rubuta, kuma ta hanyarsa ne ake samun ilimin sanin Allah da yadda za a bauta masa.

3706893

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: