Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a yau ne aka sanar da sakamakon karshe na gasar kur'ani mafi girma ta duniya akasar Malaysia tare da halartar sarkin kasar.
Wakilin Iran Mukhtar Dehqan shi ne ya zo na biyu a bangaren kira'a a wannan gasa.
Mukhtar Dehqan dai ya gudanar da karatunsa na karshe nea ranar alhamis, inda ya karanata ayoyi na 59 zuwa 66 a cikin surat nisa, kuma dukkanin alkalan gasar sun nuna gamsuwa da salon karatun nasa da kuma yadda yake kiyaye kaidoji.
Ankamala gasar wadda aka fara gudanar da ita tun a ranar Litinin da ta gabata, tare da halartar wakilan kasashen duniya fiye da hamsin.