IQNA

23:50 - May 15, 2018
Lambar Labari: 3482660
Bangaren kasa da kasa, an amince za a rika nuna fina-finan kasa Iran a kasar Senegal a zaman da kungiyar COMIAC ta gudanar a kasar.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta daga birnin Dakar cewa, a jjiya ne aka fara gudanar da zaman kungiyar bunkasa harkokin musulunci gami da al’adu ta COMIAC a kasar Senegal.

 Wannan kungiya dai tana karkashin kungiyar kasashen musulmi ne ta OIC, kuma tana gudana da lamuranta ne bisa yarjeniyoyi tsakanin kasashen musulmi.

Sayyid Muhammad Hussain Hashemi mataimakin ministan kula da harokin ala’adu na Iran, da kuma Sayyid Hassan Ismati shugaba ofshin yada al’adu na Iran Senegal, suna daga cikin mahalarta taron.

A wannan zaman taron dai ana tattauna muhimman batutuwa ne da suka shafi kasashen musulmi, da kuma samar da hanyoyi na kara bunkasa alaka ta al’adu da ilimi a tsakaninsu.

Taken taron da shi ne, yada al’adu da ilimi da kuma tabbatar da sulhu a tsakanin dukkanin muuslmi da sauran al’ummomi.

3714822

 

 

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، COMIAC ، Dakar ، senegal ، IQNA
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: