IQNA

23:51 - May 19, 2018
Lambar Labari: 3482674
Bangaren kasa da kasa, an bude tafsirin kur’ani mai tsarki a kasar Ghana.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, tun daga ranar farko da aka dauki azumin watan Ramadan mai alfarma a kasar Ghana a ranar Ahamis da ta gabata, aka bude tafsirin kur’ani a masallacin Ahlul bait (S) da ke garin Tamale a arewacin kasar ta Ghana.

Sheikh Abdulmumin Dalahu shi ne babban limamin Juma’a na wannan masallaci, uma shi ne yake gabatar da karatun kur’ani da tafsiri a kowace shekara a wannan masallaci.

A bayaninsa na farko shehin malamin ya fara bayyana matsayin kur’ani mai tsarkia a matsayin wata babbar kyauta maras misiltuwa daga Allah madaukakin sarki zuwa ga bayinsa, ta hanyar masoyinsa fiyayyen halitta manzon Allah tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi da alayensa.

Haka nan kuma tafsirin na bana wanda aka tashi daga surat Kahaf da aka taya a bara, ya fara d bayanin falalolin da ke tattare da wannan sura mai albarka.

3715648

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، fara ، falalolin ، bara ، alayensa ، IQNA
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: