Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na cibiyar yada al’adun musulunci cewa, a jiya an girmama wadanda suka gudana da gasar kur’ai mai tsarki ta kasar Saliyo abirnin Freetown fadar mulkin kasar.
A yayin taron na jiya an bayar da kyautuka ga dukkanin wadada suka halarci wannan gasa, da kuma kyautuka na musamman ga wadanda suka nuna kwazo.
Ali Reza Faramarzi shugaban karamin ofishin jakadancin Iran shi ne ya bude taron da karatun surat qadr.
Kasar Iran ce dai ta dauki nauyin dukkanin abubuwan da aka kasashe a yayin gudanar da wannan gasar kur’ani ta kasar Saliyo.
Maisami Zadeh shugaban jami’ar almustafa a kasar ya bayyana cewa, wannan gasa tana da matukar muhimmanci.
Haka nan kuma an nuna karatun wasu daga cikin fitattun makaranta kur’ani Iraniyawa da suka hada da Jawad Forughi.