IQNA

22:26 - June 03, 2018
Lambar Labari: 3482721
Bangaren kasa da kasa, Musa Abdi shugaban yankin Somaliland ya halarci wurin taron kammala gasar kur’ani mai tsarki ta yankin da ake gudanarwa a kowace shekara.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Hamza Muhammad Yasin shi ne ya zo na daya a wannan gasa, inda ya samu kyautar motar Toyta sabuwa.

Sai kuma Ahmad Farah shi ne ya zo na biyu, wanda ya sau kyautar dala dubu da dari uku da na’ura mai kwakwalwa labtop.

Hamza Usman Abdullahi da kuma Samatar Nasir Hassan su ne suka zo matsayi na uku, an ba dala dubu daya kowannensu da kuma wayar salula sabuwa.

Shekaru shida kenan a jere ana gudanar da wannan gasa, wadda shugaban yankin na Somaliland n da kansa ya yake daukar nauyin gasar.

Yankin daiya sanar da ballewa tare da zama mai cin gishin kai ne tun a cikin shekara ta 1991, sakamakon rikice-rikicen da kasar take dfama da su.

3720068

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، shekara ، ballewa ، halarci
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: