IQNA

Za A Gudanar Da Zama Kan Taron Arbain Na Wannan Shekara

23:49 - June 29, 2018
Lambar Labari: 3482795
Bangaren kasa da kasa, za a gudanar da wani zaman taron karawa juna sani na kasa da kasa kan taron arbain na wannan shekara a Karbala.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya ahbarat cewa, bangaren hulda da jama'a na hubbaren Hussaini ya sanar da cewa, ana shirin gudanar da wani zaman taron karawa juna sani na kasa da kasa kan taron arbain na wannan shekara a Karbala mai alfarma.

Taron zai samu halartar malamai da masana daga kasashen duniya, wadanda za su gabatar da kasidu da suke dauke da shawarwari da mahangarsu kan batun taron da kuma yadda za a kara inganta tsarinsa.

Babbar manufar hakan dai ita ce mayar da wannan lamari ya zaman a dukkanin musulmi ne baki daya, ta yadda kowane bangare na musulmi za su shiga cikinsa domin kara samun fahimtar juna da hadin kai tsakanin dukkanin al'ummar musulmi na duniya baki daya.

Haka nan kuma bayanin ya ce za a yi amfani da damar haduwar miliyoyin musulmi a wannan hubbare mai tsarki, domin karfafa zaman lafiya a duniya, da fadakar da musulmi muhimamncin hakan, ta yadda za a fito da surar musulunci ta hakika kamar yadda take a idon duniya.

3726191

 

 

captcha