IQNA

23:47 - August 04, 2018
Lambar Labari: 3482861
Bangaren kasa da kasa, A yau jiragen yakin Isra'ila sun kaddamar da hare-hare a kan wasu yankuna na zirin Gaza.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, jiragen yakin na Isra'ila sun harba makamai masu linzami a arewacin yankin zirin Gaza a yau.

Mai magana da yawun rundunar sojin IsrailaAfikhai Ardai ya ce sun kaddamar da hare-haren a kan wasu matasa da suke harba balon-balon da ke dauke da wuta zuwa matsugunnan yahudawa da ke kusa da yankin zirin Gaza.

Babu wasu bayanai daga mahukunta a Gaza kan asarar da aka samu sakamakon hare-haren na yau da jiragen yakin Isra'ila suka kai a yankin.

3735785

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: