IQNA

23:56 - August 08, 2018
Lambar Labari: 3482873
Bangaren kasa da kasa, domin tabbatar da tsaro ga tawagar maniyyata daga kasar Ghana gwamnatin kasar ta dauki matakai na musamman.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, gwamnatin kasar Ghana ta dauki matakai na musamman domin tabbatar da tsaro ga tawagar maniyyata da suka tafi sauke farali a bana.

Daga cikin irin wadannan matakai har da tura jami’an tsaro hamsin da biyar a cikin tawagar alhazan domin gudanar da aikin tsao da kuma ba su kariya.

Shugaban kwamitin aikin hajji na kasar Ghana ya bayyana cewa, ya zwa alhazan kasar sun isa kasar Saudiyya domin sauke farali a aikin hajin bana.

Ya kara da cewa alhazan kasar za su kasance masu da’a da biyayya ga dukkanin abin da aka shata musu na kaidoji, domin su bayar da kyakkyawan wakilci ga kasar.

3736930   

 

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، Ghana ، maniyyata ، alhazai
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: