IQNA

23:48 - August 10, 2018
Lambar Labari: 3482881
Bangaren kasa da kasa, dakarun Gwagwarmayar Palastiwa sun mayar da martani kan hare-haren da jiragen yakin Sahayuna suka yankin zirin gaza, daga daren jiya laraba zuwa wayewar yau alhamis, sun harba rokoki fiye da dari biyu zuwa yankunan yahudawa 'yan kama wuri zauna dake kudancin Palastinu.

 

Kamfanin dillancin labaran iqn aya habarta cewa, kungiyar gwagwarmayar Palastinawa ta sanar da harba rokoki akalla dari biyu da ashirin zuwa yankunan yahudawa 'yan kama wuri zauna dake kudancin palastinu daga daren jiya laraba zuwa safiyar yau alhamis, lamarin da ya yi sanadiyar jikkatar sojojin sahayuwa sha daya da kuma sanya tsoro a zukatan yahudawan, inda suka nemi mafuka a cibiyoyin agaji.

Kungiyar ta Hamas ta ce ta halba rokokin ne a sansanin sojojin haramtacciyar kasar Isra'ila da kuma kauyukan yahudawa 'yan kama wuri zauna dake kan iyaka da yankin zirin gaza a matsayin mayar da martani.

A bangare guda, a wannan Alhamis jiragen yakin Haramtacciyar kasar Isra'ila sun sake kai hare-hare a yankunan Arratisi na arewa maso yammaci da yarmuk gami da Askalan dake kudancin yankin zirin Gaza.

A ranaikun talata da laraba da suka gabata, jiragen yakin sahayunan sun ruwan bama-bamai a yankin zirin gaza, lamarin da ya yi sanadiyar shahadar Palastinawa uku da kuma jikkata wasu da dama na daban.

3737192

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، Gaza ، yankin ، palastinu ، isra’ila
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: