IQNA

23:38 - August 11, 2018
Lambar Labari: 3482882
Bangaren kasa da kasa, a gobe za a gudanar da wani zaman taro mai taken tarbiya da kuma sanin Imam Zaman a garin Kuita na kasar Pakistan.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, wannan taro za a gudanar da shin a tsawon kwana daya kawai, tare da halartar daliban makarantun mabiya mazhabar Imamiya, da kuam daliban jami'a masu bukata.

Haka nan kuma an gayyaci wasu daga cikin malaman addini na yankin, da kuma wasu masana wadanda su ma za su iya gabatar da tasu mahangar a kan mauduin taron.

Daga cikin abubuwan da taron zai dubi a kansu baya ga batun tarbiyya da kuma sani Imam zaman,a kwai nazari kan matsayin wilayar malami faqihi.

3737471

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، wadanda ، ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: