IQNA

23:43 - August 23, 2018
Lambar Labari: 3482917
Bangaren kasa da kasa, An sallami babban malamin addinin muslunci na kasar Bahrain daga asibiti a birnin London, bayan jinyar da ya yi tsawon kimanin kwanaki 50, biyo bayan wani aikin tiyata da aka yi masa.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Tashar Lu'ulu'a ta bayar da rahoton cewa, a jiya tawagar likitoci masu kula da lamarin lafiyar Ayatollah Sheikh Isa Kasim sun sanar da cewa, an sallami malamin daga asibiti, inda yanzu haka yake zaune a wani wuri a birnin London, kuma zai ci gaba da zuwa asibitin lokaci zuwa lokaci domin duba lafiyarsa.

Masarautar mulkin kama karya ta kasar Bahrain ta tsare Sheikh Isa Kasim a cikin gidansa har tsawon kusan shekaru biyu duk kuwa da rashin lafiyar da yake fama da ita, amma daga karshe sakamakon matsin lambar duniya, ta bari an fitar da shi zuwa asibiti a London.

Masarautar kama karya ta kasar Bahrain ta zargin malamin da goyon bayan masu fafutukar neman hakkokinsu da aka haramta musu a matsayinsu na 'yan kasa a kasar ta Bahrain.

3740718

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: