IQNA

Shirin Fadada Birnin Makka Da Wuraren Ziyara

23:45 - August 23, 2018
Lambar Labari: 3482918
Bangaren kasa da kasa, ana shirin fadada binin Makka da wuraren ziyara da suke cikin birnin daga nan zuwa 2019.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin yada labarai na TRT ya habarta cewa, Khalid Faisal magajin garin birnin Makka ya sheda cewa, ana shirin fadada binin Makka da wuraren ziyara da suke cikin birnin na Makka.

Bayanin ya ci gaba da cewa yanzu haka akwa shirye da aka fara aiwatar da su da nufin ganin an cimma burin da aka saya a gaba na shekara ta 2030, inda adadin alhaza da za su rika sauke farali zai kai miliyan a kowace shekara.

Haka nan kuma ya kara da cewa, ana fatan ganin da zuwa shekaru sha biyu za a rika yin amfani da dukkanin hanyoyi na kimiyya da fasaha ne a wajen aikin hajji.

3740828

 

 

 

 

captcha