IQNA

23:57 - August 28, 2018
1
Lambar Labari: 3482933
Bangaren kasa da kasa, gwamnatn kasar China bata amince da dorawa gwamnatin Myanmar alhakin kisan muuslmin kasar ba.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, kamfanin dillancin labaran Reuters ya habarta cewa, China ba ta gamsu da rahoton da kwamitin kare hakkin bil adama na majalisar dinkin duniya ya fitar ba, wanda yake dora alhakin kisan musulmin Myanmar a kan sojojin gwamnatin kasar.

A lokain da take asa tambayoyin manema labarai, mai magana da yawun gwamnatin China Huwa Chinying a yau Talata, a lokacin da aka tambaye ta kan rahoton kwamitin kare hakkokin bil adama na majalisar dinkin duniya kan kisan kiyashin musulmin Rohingya, wanda aka zargi sojojin gwamnatin kasar da aikatawa, ta bayyana cewa wannan zargi ba shi ne mafita ba.

Kasar China wadda take bin addinin buda, tana da kyakkyawar alaka da gwamnatin kasar Myanmar wadda ita ma take bin addinin na buda.

Ga dukkanin alamu China za ta hana daukar duk wani mataki na ladabtarwa a kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya kan gwamnatin Myanmar an kisan musulmin Rohingya.

3742114

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، myanmar ، alhakin ، China ، rohingya
Wanda Aka Watsa: 1
Ana Cikin Dubawa: 0
Ba A Iya Watsa Shi: 0
Ahmad muhammad baba
0
0
Chinanma ai duk kafiraine don sun fadi haka. Ai suma suna kashe musulman na china din saboda haka duk aikin su iri dayane.
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: