IQNA

23:51 - August 31, 2018
Lambar Labari: 3482940
Bangaren kasa da kasa, Kungiyar kasashen muuslmi ta yi Allawadai da kakkausar murya, dangane da gasar zanen batunci a kan addinin muslunci da wasu masu kiyayya da addinin muslunci suka shirya a kasar Holland.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, A cikin bayanin da kungiyar kasashen musulmin ta fitar ta bayyana cewa, gudanar da wannan gasa na a matsayin babban cin zarafi mafi girma ne ga dukkanin musulmi biliyan 1.6 da suke rayuwa a duniya.

Dan majalisar dokokin kasar Holland Geert Wilders mai tsananin kiyayya da addinin mulunci shi ne ya shirya gasar ta  zane-zanen batunci a kan manzon Allah (SAW).

Kungiyar kasashen musulmin ta bukaci gwamnatin kasar Holland da ta hana gudanar da wannan gasa, domin hakan baya daga cikin hakkin bayyana raayi ko fadar albarkacin baki ta hanyar yin batunci ga addini ko akidar wasu.

 

3742332

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، batunci ، murya ، batunci ، shirya
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: