IQNA

23:55 - September 20, 2018
Lambar Labari: 3482998
Bangaren kasa da kasa, daruruwan mabiya mazhabar shi’a sun gudanar da jerin gwanon Ashura a kasar Sweden.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, mabiya mazhabar shi’ar ahlul bait (AS) sun gudanar da tarukan tunawa da zagayowar ranar Ashura a kasar Sweden.

Bayanin ya ce kamar kowace shekara an fito a kan tituna dauke da tutoci da kwalaye da aka yi rubutu kansu da ke bayyana abin da ya faru da Imam Hussain (AS) da kuma zuriyar manzon Allah a rana Ashura.

Bayan nan kuma an gudanar da jawabai inda muuslmi da dama suka taru mabiya mazhabar shi’a da ma wadanda ba su ba, har da wasu daga cikin turawan kasar, inda suka saurari jawaban da aka gudanar kan wannan rana.

3748469

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: