IQNA

Dakarun Ansarullah Sun kai Harin Ramuwar Gayya A Kan Filin Jirgin Dubai

23:33 - September 30, 2018
Lambar Labari: 3483022
Bangaren kasa da kasa, Dakarun kasar Yemen sun sake kai harin ne da makami mai linzami a yau a kan babban filin sauka da tashin jiragen sama na birnin Dubai cibiyar kasuwanci ta UAE.

Kamfanin dillancin labaran iqna, wannan hari da dakarun na Yemen suka kai a karo na biyu a yau, sun kai shi ne da makami mai linzami wanda jirgi maras matuki samfurin Sammad 3 ya harba, bayan wani harin makamancinsa da suka kai a safiyar yau.

Dakarun na Yemen sun sanar da cewa wannan somin tabi ne matukar UAE da Saudiyya ba su dakatar da kisan kiyashin da suke yi a kan kasar Yemen ba, domin kuwa duniya ta zura ido tsawon shekaru uku ba tare da wani ya ce uffan ba, saboda haka al’ummar Yemen za su kare kansu ta hanyoyin da suke ganin sun dace.

Kasashen Saudiyya da UAE dai sun fara kaddamar da hare-hare kan kasar Yemen ne tun kimanin shekaru uku da suka gabata, inda suka kashe dubban faren hula bisa rahotani na majalisar dinkin duniya.

3751302

 

 

 

 

captcha