IQNA

23:50 - October 06, 2018
Lambar Labari: 3483030
Bangaren kasa da kasa, kwamitin mabiya addinin muslunci a kasa Afrika ta kudu MJC ya yaba da kame mutane uku da ake zargi da kai kan masallacin Imam Hussain (AS).

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habata cewa, musulmin Afrika ta kudu sun damuwa matuka dangan da yadda suka ga gwamnati ba ta dauki matakai na kame mutanen da suka kai harin ba, amma bayan daukar wannan mataki a cikin wannan mako, sun yaba da hakan.

A cikin watan azumin da ya gabata ne wasu mutane suka kai hari kan masallacin Imam Hussain (AS) da ke cikin gundumar Dauban, inda suka kasha limamin masallacin tare da jikkata wasu masallata.

Yanzu haka dai mutanen da aka kam suna hannun jami’an tsaro ana gudanar da bincike a kansu, duk kuwa da cewa a lokuta daban-daban sun yi ta yin barazanar kai harin a kan masallacin, har ma da yin barazanar saka bam a wata kasuwa ta musulmi da ke kusa da masallacin.

3753304

 

 

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: