IQNA

23:08 - October 15, 2018
Lambar Labari: 3483041
Bangaren kasa da kasa, An gudanar da babban taron jami’ar musulunci ta kasar Ghana a daidai lokacin da ake komawa zangon karatu a jami’ar.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Kamar kowace shekara a lokacin da aka dawo karatu, jami’ar ta kan dauki nauyin shirya wani taro wanda zai hada dukkanin malaman jami’ar da kuma wasu masana daga waje.

A yayin gudanar da taron a kan tabo muhimman lamurra da suka shafi bincike na ilimi a bangarori daban-daban, da kuma irin abin da ya kamataal’umma ta amfana da shi abangaren bincike musamman a kan ilmomi masu sarkakiya, kamar falsafa da sauransu.

Taron an wannan shekarar dai ya samu halartar manyan malaman addinin muslunci da kuma wasu masana da aka gayyata daga wasu jami’oi na ciki da wajen kasar ta Ghana.

Jami’ar muslunci ta Ghana tana kara fadada bangarorin da ake gudanar da kwasa-kwasai a kansu, baya ga kwasa-kwasan da suka danganci addinin musulunci.

3755950

 

 

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، komawa ، gudanar ، ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: