IQNA

An fara Wani Bayar Da Horo Kan Sanin Musulunci A Zimbabwe

23:57 - October 20, 2018
Lambar Labari: 3483059
Bangaren kasa da kasa, an fara gudanar da wani shiri na bayar da horo kan sanin addinin muslunci a kasar Zimbabwe.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin yada labarai na cibiyar yada al’adun muslunci ya bayar da rahoton cewa, a jiya ne aka fara gudanar da wani shiri na bayar da horo kan sanin addinin muslunci a kasar Zimbabwe tare da hadin gwiwa da jami’ar Qom.

Bayanin ya ce wannan shiri yana gudana ne a daidai lokacin da ake kara samun ci gaba ta fuskar bincike kan addinin muslunci a kasar Zimbabwe, yayin dakuma ake samu masu karbar addinin mulsunci sakamakon bincikensu.

Dukkanin wadanda suke halartar wannan shirti dai daliban jami’a ne, daga cikinsu akwai wadanda suke yi karatu digiri na farko, akwai masu karatun digiri na biyu.

Shirin ya hada da laccoci kan wasu muhimman lamurra da suka shafi addinin musulunci, da kuma amsa tambayoyi kan mulsunci.

3757155

 

 

 

captcha