Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin yada labarai na Albawwabah News cewa, bisa wani bincike da wata cibiyar bincike ta gudanar a kasar Aljeriya, kan adadin malaman kur’ani maza da mata a kasar, ya nuna cewa addain malaman kur’ani maza ya ragu idan aka kwatanta da mata.
Saikamakon binciken ya nuna cewa adadin maza masu koyar da kur’ani a makarntu kama daga na zamani har zuwa na gargaji ko kuma na allo, ya nuna cewa adadin ya ragu idan aka kwatanta da loktan baya.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da adadin mata masu koyar da kuyr’ani makarantu ya karu fiye da kowane lokaci a tarihin kasar.
Wannan lamari ya sanya cibiyoyin kur’ani suka fara tunanin gano dadlilan da suka jaza hakan, musamman ma ganin cewa mafi yawan daliban da makarantunsuke yayewa musamman wadanda suka yi karatu mai zurfi maza ne.