IQNA

23:40 - October 22, 2018
Lambar Labari: 3483065
Bangaren kasa da kasa, an ci gaba da gudanar da aikin gyaran masallacin Zaher Bibris da ke birnin Alkahira bayan tsawar aikin tun shekaru bakawai.

Kamfanin dillancin labaran iqn aya habarta cewa, shafin yada labarai Rasha ya habarta cewa, an ci gaba da gudanar da aikin gyaran masallacin tarihi na Zaher Bibris da ke birnin Alkahira na kasar Masar, wanda aikin gyaransa ya tsaya tun 2011.

Wannan aiki dai zai dauki tsawon watanni 12 zuwa 18 ana gudanar da shi kafin a kammala shi, kamar yadda kuma zai lakume kudi kimanin fam miliyan daya da rabi.

An gina masallacin ne a lokacin Sarki Zaher Bibris bin Abdullah Bandkaddari a cikin shekarar 665 zuwa 667 bayan hijira manzon Allah.

Haka nan kuma an gudanar da gyaransa a cikin shekara ta 1893, kuma tun daga wannan lokacin ne aka sanya a shi a cikin muhimman wurare na tarihin kasar Masar.

3757849

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، Alkahira ، masar ، kammala
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: