Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Akon fitaccen mawaki dan kasar Amurka kuma dan asalin kasar Senegal ya bayyana shirinsa na tsayawa takarar shugabancin kasar Amurka domin kalubalanta shugaba mai ci yanzu.
Akon dai ya shara wajen nuna tsananin kiyayya da salon siyasar wariya da bangaranci irin ta Donald Trump, kuma ya sha alwashin cewa idan har lashe shugabancin Amurka, to za a kawo karshen irin wannan bakar siyasa ta Trump.
A cikin shekarun baya dai Akon ya gina makarantu a wasu daga cikin kasashen nahiyar Afrika, domin taimaka ma marassa karfi.