Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Bakwai daga cikin mutanen sun mutu sai kuma wasu 14 da su ka jikkata.
Tashar talabijin din al-Mayadeen ta ambato limanin kiristoci kibdawa na yankin Minya yana cewa; An kai wa mutanen hari a lokacin da suke kan hanyarsu ta zuwa gundumar Suhaj.
Kamfanin dillancin labarun Reuters kuwa ya ce an kai harin ne a kusa da majami'ar Saint Samuel da take a gundumar Minya.
Kawo ya zuwa yanzu babu cikakken bayani akan wadanda su ka kai harin da kuma manufarsu.
A cikin shekaru biyu na bayan nan an kai irin wannan harin akan mabiya addinin kirista a cikin kasar ta Masar wanda ya ci rayukan fiye da mutane dari.
Masar na fama da matsalar ta'addanci da kungiyoyi masu dauke da makamai suke kai hare-hare.