IQNA

Zaman Taro Mai Taken Musulunci Addinin Rahma A Zimbabwe

23:53 - November 13, 2018
Lambar Labari: 3483123
Bangaren kasa da kasa, an shirya gudanar da zaman taro mai taken musulunci addinin rahma a kasar Zimbabwe.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a jiya an gudanar da zaman taro mai taken musulunci addinin rahma a birnin Harare fadar mulkin kasar Zimbabwe.

Ofishin jakadancin kasar Iran a Zimbabwe ne ya dauki nauyin shirya wannan taro da kuma gudanar dashi, a daidai lokacin da ake gudanar da tarukan shigowar watan Maulidin manzon Allah (SAW).

A wannan taron an gayyaci malaman addinin muslunci na sunna da shi’a da darikoki, kamar yadda kuma an gayyaci malaman addinin kirista, wadanda suke zaune lafiya tare da muuslmi a kasar.

An gabatar da jawanai kan tarihin manzon Allah da kuma irin darussan da rayuwarsa take koyar da dan adam, ta fuskar hakuri, tausayi, taimakon marassa galihu, gudun duniya, gaskiya da rikon amana da dai sauransu.

 

3763740

 

 

captcha