IQNA

20:41 - November 19, 2018
Lambar Labari: 3483135
Bangaren kasa da kasa, musulmin kasar Canada suna gudanar da tarukan maulidin manzon Allah a birnin Calgray.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafukan yada labarai na garin Calgray sun bayar da bayanin cewa, kwamitin kula da harkokin musulmi na birnin ya raba sakonni na gayyata zuwa taron Maulidin manzon Allah (SAW).

Bayanin ya ce yanzu haka kwamitin musulmin shi ne yake daukar nauyin dukkanin shirye-shiryen taron wanda yake gudana, wanda shi ne taro mafi  irinsa mafi girma da musulmin birnin suke gudanarwa a birnin.

Taron yana samu halartar musulmi mazauna birnin, da kuma wasu wadanda aka gayyata wadanda ba musulmi ba, da suka hada da mabiya addinai daban-daban.

Haka nan kuma wasu daga cikin malaman addinin kirista inda ake gabatar da jawabi akan matsayin manzon Allah (SAW) da kyawawan halayensa da dabiunsa, wadanda suke abin koyi ne ga dukkanin 'yan adam, musulmi da ma wadanda ba musulmi ba.

Kamar yadda kuma za a kara karfafa muhimmancin fahimtar juna tsakanin musulmi da ma wadanda ba musulmi, kamar yadda musulinci ya koyar kuma yake karfafa hakan.

3765018

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: