IQNA

23:31 - November 24, 2018
Lambar Labari: 3483147
A yau ne aka bude babban taron makon hadin kan al'ummar musulmi a birnin Tehran na kasar Iran, tare da halartar masana daga kasashe 100 na duniya.

Kamfanin dillancin labaran iqna, 

Taron wanda ake gudanar da shi a karo na 32 da ake gudanarwa a kowace shekara, a wannan karon yana da taken "Quds Mahadar Al'ummar Musulmi" inda shugaba Hassan Rauhani ne ya bude taron da jawabinsa.

A cikin jawabin nasa shugaba Rauhani ya bayyana cewa, babbar matsalar al'ummar musulmi a halin yanzu ita ce rashin hadin kai da ke tsakaninsu, wanda hakan ne ya baiwa makiya musulunci damar samun shimfida ikonsu a kan kasashen musulmi.

Rauhani ya kara da cewa, yahudawa da Amurka, sun samu damar nisantar da wasu daga cikin larabawa da na musulmi daga batun Palastinu da kuma masallacin Quds, inda suke kokarin bayyana Iran a matsayin ita ce hadari gare su, domin su yi amfani da hakan wajen yin cinikin makamai a tsakanin kasashen larabawa.

Daga karshe shugaba Rauhani ya jaddada cewa, Iran a shirye take ta hada kai da dukkanin kasashen musulmi musamman na larabawa da ke yankin gabas ta tsakiya domin tabbatar da tsaro a yankin baki daya.

3766535

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، hada kai ، tabbatar
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: