IQNA

An Yi Jerin Gwanon Goyon Bayan Al’ummar Palastine A Najeriya

23:41 - December 17, 2018
Lambar Labari: 3483224
Bangaren kasa da kasa, wasu daga cikin mutanen Najeriya sun gudanar da jerin gwano domin nuna goyon baya ga al’ummar Palastine.

Kamfanin dillancin labaran iqna, kamfanin dillancin labaran Anatoli ya bayar da rahoton cewa, a jiya daruruwan mutanen birnin Uyo na jahar Osun a Najeriya ne suka gudanar da jerin gwano domin nuna goyon baya ga al’ummar Palastine.

Masu gangamin sun yi kira ga majalisar dinkin duniya da ta amince da kasar Palastine mai cin gishin kanta, tare da yin tir da Allawadai da irin cin zalun da Isra’ila take yi al’ummar Palastine.

Sheikh Dawud Umar Mulla Hassan na daga cikin wadanda suka jagoranci gangamin, ya kuma bayyana cewa al’ummar Najeriya basa goyon bayan zaluncin da ake yi wa Falastinawa, a kan suna kira ga majalisar dinkin duniya da sauran kasashen duniya, da su sauke nauyin da ke kansu na kare al’ummar Palastine.

3773061

 

 

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، falastinawa ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha