IQNA

Belgium: An Hana Musulmi Yanka Dabbobi Bisa Tsari Na Musulunci

22:51 - January 02, 2019
Lambar Labari: 3483276
Majalisar jahar Felmish a kasar Belgium ta kada kuri'ar amincewa da daftarin doka, wanda ya hana yanka dabbobi bisa tsari irin na musulunci.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a Majalisar jahar Felmish a kasar Belgium ta kada kuri'ar amincewa da daftarin doka, wanda aka gabatar a gaban majalisar tun a cikin shekarar da ta gabata, wanda hana yanka dabbobi bisa tsari irin na musulunci, matukar dai ba asumar da dabba ba kafin yanka ta.

Wannan daftarin doka masu rajin kare hakkokin dabbobi a kasar Belgium ne suka gabatar da shi, bisa hujjar cewa ana cutar da dabba kafin ta mutu a lokacin da ake yanka ta, a kan suka buka ci a kafa dokar da za ta tilasta a somar da dabba kafin yanka, sabanin yadda musulmi suke yi.

Musulunci dai yana da nasa tsari a kan batun yanka, daga ciki kuwa har da kasancewar dabbar da za a yanka ta zama a farke a some ba, kuma alokacin da zuciyarta take bugawa, domin jinin da ke jikinta ya fita baki daya.

Wasujahahi a kasar ta Belgium na da shirin aiwatar da irin wannan doka, inda a cikin watan Satumban wannan shekara ta 2019, ana sa ran majalisar dokokin jahar Valonia za ta amince da doka makamnciyar wannan.

Wasu kasashen turai ma tuni suka dauki matakin takura musulmi kan gudanar da yankan dabbobi bisa tsari na musulunci, daga ciki kuwa har da Danmark, Sweden, New Zealand, da kuma Holland.

3777849

 

captcha