IQNA

23:42 - February 05, 2019
Lambar Labari: 3483348
Bangaren kasa da kasa, babban sakataren kungiyar gwgawarmayar Musulunci ta Lebanon Sayyid Hassan Nasarallah ya bayyana haka ne a jiya da dare da ya gabatar da jawabi akan kafa sabuwar gwamnatin kasar Lebanon

Kamfanin dillancin labarn iqna, Sayyid Hassan  Nasarullah ya kara da cewa; Juyin musulunci wanda Imam Khumain ya jagoranta ya haifar da gagarumin sauyi  a cikin yankin gabas ta tsakiya, ya kuma farkar da al'umma da kungoyoyin gwgawarmaya

Babban sakataren kungiyar ta Hizbullah ya kuma kara da cewa; A wurinmu juyin musulunci na Iran yana da matukar muhimmanci domin yana da alaka da makomar yankin gabas ta tsakiya, da Palasdinu da gwgawarmaya da kuma tarihinmu da cigabanmu.

Sayyid Nasarllah ya yi ishara da makirce-makircen da Amurka ta rika kitsawa juyin musulunci sai dai ba ta yi nasara ba, kamar yakin da ta kallafawa Iran ta hanyar Saddam na Iraki.

Da yake magana akan kafa sabuwar gwamnati a Lebanon ya ce; Da akwai bukatar zaman lafiya da kwanciyar hankali domin kare manufofin kasa da kuma warware matsalolin da kasar take fuskanta

A ranar 31 ga watan January ne dai aka kafa sabuwar gwmanatin bayan gushewar watanni 9 daga yin zabe.

3787602

 

 

 

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: