IQNA

23:06 - February 16, 2019
Lambar Labari: 3483378
Bangaren kasa da kasa, Muhammad Abdulfadil Al-shusha gwamnan lardin Sinai ya bayyana cewa nan ba da jimawa ba za a gudanar da gasar hardar kur’ni ta lardin.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, sheikh Muhammad Al-ush babban daraktan ma’aikatar kula da harkokin addini a lardin Sinai shi ma a nasa bangaren ya sanar da hakan, inda y ace a farkon watan Maris mai kamawa ne za a fara gudanar da gasar, wadda za ta zauki tsawon mako guda.

Haka nan ya kuma ya bayyana cewa, wanna gasa za ta kunshi bangarori daban-daban nagasar hardar kur’ani mai tsarki.

Duk kuwa da cewa dai wannan shi ne karon farko da za a gudanar da irin wannan gasa a mataki na lardin baki daya, amma tuni an kammala dukkanin shirye-shiryen da suka kamata a cewarsa.

Haka nan kuma an ayyana sunayen da suka yi rijista domin shiga gasar, wadda za ta samu halartar wakilai daga sassa na kasar ta Masar.

3790494

 

 

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، halartar ، Sinai ، Masar
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: