IQNA

23:49 - February 19, 2019
1
Lambar Labari: 3483386
Bangaren kasa da kasa, miliyoyin musulmi a kasar India a birane daban-daban sun yi zanga-zangar nuna adawa da ziyarar Muhammad birnin Salman a kasar.

Kamfanin dillancin labaran iqna, a yau musulmi a kasar India a birane daban-daban sun yi zanga-zangar nuna adawa da ziyarar Muhammad birnin Salman da aka shirya zai kai yau a kasarsu.

Wannan zanga-zanga an gudanar da irinta  akasar Pakistan a ranar 17 ga wannan wata Fabrairu da akshirya cewa yariman Saudiyya zai kai ziyara a kasar, wanda hakan yasa ala tilas aka dage ziyarar zuwa ranar 18 ga wata.

An dai shirya cewa  ayau Bin Salman zai nufi kasar India, amma a can ma dai zanga-zangar ta fara gabatar zuwan nasa, inda wanda kuma musulmi ne suke gudanar da zanga-zangar nuna adawa da ziyarar tasa.

Babban abin da yasa Bin Salman ke fusntar zanga-zanga duk inda ya nufa a halin yanzu a duniya shi ne kisan Jamal Khashoggi, da kuma hannun da yake da shi a kisan al’ummar kasar Yemen.

3791639

 

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، zanga-zanga ، amma ، India ، Bin Salman
Wanda Aka Watsa: 1
Ana Cikin Dubawa: 0
Ba A Iya Watsa Shi: 0
Ba A San Shi Ba
0
0
saima yaje lahira zai gane kuskurensa in bai tubaba
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: