Mas’ud Shajareh shugaban kungiyar kare hakkokin musulmia Birtaniya ya bayyana cewa, babu wata doka da gwamnatin Birtaniya ta dogara da ita a cikin kundin tsarin mulkin kasar wajen haramta Hizbullah.
A bangaren babbar jami'a mai kula da harkokin siyasar wajen kungiyar tarayyar turai Federica Mogherini ta bayyana cewa; matakin da gwamnatin Birtaniya ta dauka dangane da kungiyar Hizbullah ya shafi kasar Birtaniya ne kawai, amma bai shafi kungiyar tarayyar turai ba.
A jiya ne ministan cikin gida na kasar Birtaniya Sajid Jawid ya yi da'awar cewa, kungiyar Hizbullah tana haifar tashe-tashen hankula a cikin kasashen yankin gabas ta tsakiya, ba tare da yin ishara da wata kasa guda daya da hakan ya faru ba, a kan haka ya ce sun dauki matakin haramta kungiyar tare da saka ta a cikin kungiyoyin 'yan ta'adda.
A nasa bangaren shugaban kasar Faransa Emmanuel macron ya bayyana matakin an Birtaniya da cewa ba za su amince da shi ba, domin kuwa Hizbullah tana da wakilci a cikin gwamnatin Lebanon, saboda haka babu dalilin da zai sanya a kira kungiyar ta 'yan ta'adda, kuam Faransa za ta ci gaba da mu'amala da kungiyar a hukumance.
A nata bangaren Amurka ta yaba da wannan mataki na Birtaniya, tare da bayyana cewa ya yi daidai kuma tana goyon bayan hakan.