IQNA

Iran Da Phillipines Na Gudanar Ayyukan Hadin Gwiwa A Bangaren Abincin Halal

23:54 - March 04, 2019
Lambar Labari: 3483422
Gwamnatocin kasashen Iran da Philipines suna gudanar da ayyukan hadin gwiwa a bangaren samar da abincin halal.

kamfanin dillancin labaran iqna, ya habarta cewa, a wata ganawa da aka yi jiya a tsakanin jami’an Iran da na Philippines a birnin Manila bangarorin biyu sun cimma matsaya kan ayyukan hadin gwiwa  a tsakaninsu domin samar da abincin Halal.

Carmen Alviar shugabar cibiyar kula da harkokin yawon bude a kasar da kuma Marisa Alkantara mamba a kungiyar bunkasa harkokin yawon bude a kudanci da gabashin nahiyar Asia, sun gana da jami’an kasar Iran tare da sanya hannu kan yarjejeniyoyi da suka shafi samar da abincin Halal  a kasar da ma wasu kasashen nahiyar Asia.

Madam Carmen ta ce ko shakka babu kasar ta Iran ta taka gagarumar rawa wajen samar da abincin halal da ake yin amfani das hi a kasashen nahiyar asia da dama, da hakan ya hada har da kasar ta Phillipines.

Kasar Phillipines dai tana niyyar fadada ayyukan samar da abincin halal ne da nufin kara jawon hankulan musulmi daga ko’ina cikin duniya domin zuwa yawon bude ido a kasar, wanda kuma daya daga cikin hanyoyin jawo musulmi shi ne samar da abinci na halal.

3794946

 

captcha